'Yan Taliban sun sace 'yan sanda 10

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Mayakan Taliban a Afghanistan

'Yan sanda a Afghanistan sun ce kungiyar Taliban ta sace 'yan sanda akalla goma, bayan wani hari da kungiyar ta kai kan hedkwatar wata gunduma da ke yankin.

Kakakin rundunar 'yan sanda na Lardin Badakh-shan, ya shaida wa BBC cewa hudu daga cikin jami'an 'yan sanda sun mutu bayan fada ya kaure.

Lamarin ya faru ne lokacin da'yan kungiyar suka bude wa harabar gwamnati wuta a gundumar Wardoj.

Bayanai sun ce 'yan Taliban sun samu galaba duk karin jami'an tsaron da aka tura zuwa yankin.