Kwalara ta kama mutane 1,300 a Niger

Image caption Dubban 'yan Afrika na mutuwa sakamakon cutar kwalara a duk shekara

Majalisar dinkin duniya ta ce mutane fiye da 1,300 sun kamu da cutar kwalara a Jamhuriyar Niger a wannan shekarar.

Alkaluman da majalisar ta fitar sun nuna cewar mutane 51 daga cikin wannan adadin sun rasu sakamakon kamuwa da cutar.

Ofisihin majalisar dinkin duniya ya kara da cewar mutane kusan 38 ne cutar kwalara ta hallaka a cikin watan Satumbar da ta wuce.

Sannan majalisar ta nuna damuwa kan yanayin da dubban 'yan gudun hijira su ke ciki a yankin Diffa wadanda suka tsere daga rikicin Boko Haram a Nigeria.