Google zai samar da na'urar gano Kansa

Kamfanin Google Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Kamfanin Google

Kamfanin Google yana yunkurin gano cutar Kansa da ciwon bugun-zuciya da shanyewar wani bangare na jiki da sauran wasu cututtuka tun kafin cutar ta yi karfi fiye da tsarin da ake amfani da shi a yanzu.

Kamfanin yana aiki a kan wata fasaha wadda ke amfani da wasu hanyoyi na gano cuttuka dake ratsa hanyoyin jini na dan-adam ta hanyar shan kwayoyin magani da wata hanyar ta daura wata na'urar binciken cuttukan a hannun dan-adam.

Manufar yin haka shine a gano idan akwai wani dan canji a yanayin jikin dan-adam wanda zai zamo alamun farko na rashin lafiya.

Wannan yunkuri da kamfanin na Google ke yi a yanzu, bai je ko'ina ba tukuna.

Gano cututtuka, tun kafin su ci karfin mutum ita ce babbar hanyar magance su.

Cututtuka da dama na Kansa ana gano su ne kawai bayan sun ci karfin mutum, sun gama da shi, sun zamo ciwon ajali.

Burin kamfanin na Google shine samar da wata hanya ta binciken jini a kodayaushe don gano ko akwai alamun Kansa, abinda zai bayar da damar gano cutar tun kafin ta bayyana zahiri a jikin dan-adam.

Wani sashen bincike ne Google X ke gudanar da wannan binciken, sashen da musamman aka kebe don binciken wasu abubuwa na kirkiren zamani.

Wannan yunkuri na kamfanin Google alamu ne na baya-bayan nan na yadda kamfanin ya kara dulmiya ga ayyukan bincike na kiwon lafiya, bayan wasu hanyoyin da kamfanin ya kirkiro na gano ciwon suga ta hanyar amfani da wani tabarau.

Google din dai har ila yau, ya sa kafa a wani kamfanin mai binciken magungunan da za su hana tsufa da wuri da wani kamfanin 23andMe, wanda ke samar da na'urorin gwajin halayya.

Karin bayani