Satar motoci masu tsada tana karuwa

Motoci masu makullin Komputa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Motoci masu makullin Komputa

Wani kamfanin kera motoci a Brittaniya ya yi gargadin cewa, a yanzu gungun masu aikata miyagun laifukka sun fi maida kai ga motoci masu tsada dake amfani da tsari na na'ura mai kwakwalwa.

Kungiyar kamfafanoni masu kera motoci da masu tallatar da su sun ce, barayin suna tsallake tsarin tsaro na motocin ta hanyar amfani da na'urar da aka yi musamman saboda Kanikawa.

Kamfanonin kera motocin suna kokarin zarce sanin barayin ta hanyar sabunta tsarin tsaro na Komputa da aka yi ma motocin.

An ba da rahoton cewa an ki bayar da inshora ga wasu mutane wadanda ke da motocin Range Rover a London a kan wannan batu.

Wannan gargadin ya kara jaddada wani gargadin ne da hukumar binciken miyagun laifukka ta kamfanin Inshora na kasa ta Amurka ta yi, wadda tun farkon wannan shekarar tace ta lura da karuwar satar motocin nan ta hanyar amfani da wata na'ura dake lalata tsarin tsaro na motocin da ba su da makulli.

Direban motar ne ke rike wata 'yar na'ura ta bude motar da tayar da ita wadda a kan shafi motar ne kawai ta bude a kuma tayar da ta.

A yayinda ake kara kera motocin da ba su amfani da makulli, masu satar motocin suna sayen na'urar dake lalata tsarin bude su da tayar da su ta internet.

Kamfanin Jaguar Land Rover, ya ce satar motocin ta hanyar lalata tsarin tsaron su, shine ya zamo babbar matsalar kamfanonin dake kera motocin.

Kamfanin na Jaguar yace, tsarin mu yana tafiya daidai da bukatun kamfanonin Inshora a yadda aka yi gwaji da kuma daddale tsarin da kamfanonin.

Sai dai kuma kamfanin ya ce, suna daukar wannan batu da matukar muhimmanci, kuma Injiniyoyinsa suna aiki da hadin-gwiwar kamfanonin Inshora da 'yan sanda don magance wannan matsalar da ta taso.

Karin bayani