Kwankwaso ya kaddamar da neman takara

Gwamna Kwankwaso
Image caption Kwankwaso ya yi ikirarin matukar rage cin hanci da rashawa a Kano

Gwamnan jihar Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya kaddamar da aniyarsa ta neman tsaya wa takaran shugabancin kasa, a inuwar babban jam'iyyar adawa ta APC.

Kwankwaso wanda ya yi bikin kaddamarwar a Abuja, ya shaida wa BBC cewa ya samu nasarori da dama da suka zame masa tsani na zama shugaban kasa a Najeriya.

Gwamnan ya ce zai amince da sulhu a tsakanin wandanda suke neman takarar shugabancin kasar a APC, muddin an bayyana masa sharuddan da ya sa za a nemi ya janye takarar tasa.

Tuni dai tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar da tsohon shugaban mulkin soji Janar Muhammadu Buhari suka ayyana sha'awar tsaya wa takarar shugabancin kasar a inuwar jam'iyyar ta APC.

A watan gobe ne dai babbar jam'iyyar adawar za ta yi zaben fitar da gwani, domin tsayar da mutum guda da zai tsaya mata takarar shugabancin kasar, a zaben shekarar 2015 da ke tafe.

Karin bayani