PDP za ta dauki mataki a kan Tambuwal

Aminu Waziri Tambuwal Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Aminu Waziri Tambuwal

A Najeriya, jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ta maida martani kan sauya-shekar da kakakin Majalisar Wakilai, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, ya yi daga PDP zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

Shi dai kakakin Majalisar ya sanar da daukar wannan mataki ne ranar Talata a zaman majalisar, inda daga bisani kuma ya dage zamanta zuwa ranar uku ga watan Disamba.

Mataimakin kakakin Jam'iyyar PDP, Barrister Ibrahim Jallo, ya bayyana cewa Jam'iyyar PDP ba ta gamsu da hanyar da Kakakin ya bi wajen sauya-shekar ba, don haka za ta dauki mataki a kansa.

Jam'iyyar ta PDP dai na dakon sakamakon karar da ke gaban kotu game da wasu 'yan majalisar da suka sauya sheka daga cikinta zuwa APC.

Karin bayani