'Muna ci gaba da tattaunawa da Boko Haram'

Image caption Kongiyar Boko Haram ta sace mata da 'yan mata da dama a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa

Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Reuben Abati, ya ce gwamnatin kasar na ci gaba da tattauna wa da kungiyar Boko Haram.

Hakan na zuwa ne makonni biyu bayan gwamnatin ta sanar da cewa ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da kungiyar.

Ko da yake kawo yanzu ana ci gaba da kai hare-hare a wasu sassan arewa maso gabashin kasar.

Haka kuma kungiyar ba ta ce uffan game da yarjejeniyar ba, sannan ba ta sako 'yan matan Chibok fiye da 200 da take tsare da su fiye da watanni shida ba.

Lamarin dai yasa 'yan Najeriyar da dama ke nuna shakku game da cimma yarjejeniyar.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba