QPR ta tashi daga kasan tebur

QPR Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption QPR ta doke Liverpool a watan Satumba

Kungiyar Queen Park Ranger ta tashi daga kasan teburin gasar Premier bayan ta doke Aston Villa da ci 2-0.

Bobby Zamora da Eduardo Vargas ne suka zira wa QPR kwallayenta, yanzu haka kuma ta na da maki bakwai.

A baya dai QPR ta kasa samun nasarar wasannin biyar a jere kuma rabon da ta sami irin wannan nasara tun bayan da suka lallasa Liverpool a ranar 13 ga watan Satumban da ya gabata.

Yanzu haka kungiyar Burnley ce kasan teburin gasar da maki 4.