'Yan Boko Haram sun kafa tuta a Mubi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram ta kama garuruwa da dama a arewa maso gabashin Nigeria

Rahotannin da ke fitowa daga garin Mubi da ke jihar Adamawa na nuna cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kame garin, har ma sun kafa tutarsu.

Kazalika sun kafa dokar hana fita ko shiga garin, sannan a bangare guda kuma an datse layukan waya, lamarin da ya munana harkar sadarwa.

Wani dan garin na Mubi, Mallam Ahmed Sajo ya shaidawa BBC cewar lamarin ya ritsa da 'yarsa da kuma iyayensa, wadanda ya ce ya daina jin duriyarsu.

Malam Sajo ya ce "Wadannan mutanen sun kama garin, sun fasa kofar fursuna sun saki fursunoni. Sun kuma kama barikin 'yan sanda sannan sun hana mutane shigowa ko barin garin."

Ya kara da cewar "Galibin jama'ar garin sun gudu.'Yan Boko Haram suna yawo da motoci da babura a cikin garin suna ta kabbara."

Muzauna garin da dama sun bazama daji da tsaunuka don neman tsira.

Kawo yanzu hukumomi a Nigeria ba su ce komai ba game da lamarin.

Garin Mubi wanda ke kusa da iyaka da Kamaru shi ne gari na biyu mafi girma a jihar Adamawa.

A farkon watan nan, gwamnatin Nigeria ta sanar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da 'yan Boko Haram, abin da zai kai ga sakin 'yan matan Chibok su sama da 200 da 'yan Boko Haram din suka sace sama da watanni shida.