Bature ya zama sabon shugaban Zambia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Scott na masabiha da askarawan kasar

An nada mataimakin shugaban Zambia, Guy Scott, a matsayin shugaban kasar na wucin gadi don maye gurbin Michael Sata, wanda ya rasu a ranar Talata.

Darewar Mr Scott karagar shugaban Zambiyar ya sa ya zama jar fata na farko da ya zama shugaban wata kasa ta Afrika tun bayan F W de Klerk, kafin kawo karshen mulkin wariya a Afrika ta Kudu.

Zai ci gaba da mulki har zuwa lokacin da za a zabi sabon shugaban kasa a cikin abin da bai wuce kwanaki casa'in ba.

An dai kwashe watanni da dama ana rade-radi game da batun rashin lafiyar Mista Micheal Sata.

Ba a dai bayyana kowace irin cuta ce Mr Sata ya yi fama da ita ba.