Tazarce: An kona majalisar Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hayaki na fitowa daga majalisar

Masu zanga-zanga sun kutsa cikin majalisar dokokin Burkina Faso a Ouagadougou babban birnin kasar kafin kada kuri'a kan sauya kundin tsarin mulkin kasar.

Wakilin BBC a birnin ya ce masu zanga-zangar sun cinna wa ginin majalisar wuta kuma hayaki na fitowa daga cikinsa.

Tun da farko jami'an tsaro sun harba barkonon tsuhuwa don tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi wa ginin majalisar kawanya.

A ranar Alhamis ne aka shirya 'yan majalisar dokoki za su kada kuri'ar shirin gwamnati na yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, domin bai wa Shugaba Blaise Compaore damar sake tsayawa takara a shekara mai zuwa.

Mr. Compaore wanda ke kan mulkin tun a shekarar 1987 sakamakon juyin mulkin soji da ya yi, ya lashe dukkan zabukan da aka gudanar a kasar.