An sako Bajamushen da aka sace a Ogun

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matsalar tsaro babban kalubale ne ga jami'an tsaron Najeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta tabbatar da sako Bajamushen nan da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace a farkon makon nan.

A ranar Litinin ne wasu mutane suka tare Jamusawa biyu ma'aikatan kamfanin Julius Berger a wajen Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, inda suka harbi daya kuma ya mutu a kan hanyar kai shi asibiti.

Mataimakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Ogun, bai yi karin bayani ba a kan ko an kama wasu ko kuma an biya diyya kafin a sako Bajamushen ba.

Sace fararen fata tare da yin garkuwa da su ba sabon abu ba ne a kudancin Najeriya, matsalar da har yanzu jami'an tsaro suka gaza magancewa.