An samu manhajar gano masu shirin aikata laifi

London Hakkin mallakar hoto eyewire
Image caption Manhajar za ta taimaka wajen rage kudaden da rundunar 'yan sandan London ke kashewa wajen yaki da masu aikata laifuka

'Yan sanda a birnin London sun gwada wata manhaja da za ta basu damar gano wadanda ke da yuwuwar aikata laifi.

Gwajin wanda aka kwashe makwanni 20 ana yi ya kasance irin shi na farko a Burtaniya, koda ya ke an kwatanta irinsa a baya.

Yayin gudanar da binciken samar da manhajar, an yi amfani da bayanai na tsawon shekaru biyar dake kunshe da tarihin masu aikata laifuka.

Sai dai yanzu haka masu rajin kare hakkin bil adama sun fara nuna damuwarsu kan shirin fara yin amfani da wannan manhaja.

Koda yake kamfanin Accenture da ya samar da ita ya ce alfanun shirin yafi illar da ake tunanin zai iya haifarwa.

"'Yan sanda na da kudade kadan ne na gudanar da ayyukansu, saboda haka akwai bukatar a yi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka fi dacewa." In ji shugaban sashen kula da hakkokin jama'a na kamfanin, Muz Janoowalla.

Ita dai wannan manhaja, za ta iya bayyana mutane ko kuma kungiyar dake shirin aikata wani laifi ne.

"Manhajar za ta iya sa 'yan sanda su fi mayar da hankalinsu kan wadanda ake ganin suna shirin aikata wani laifi." Janoowalla ya kara da cewa.