'Yan Boko Haram sun fasa bankuna a Mubi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan Boko Haram su lalata dukiya ta miliyoyi a Nigeria

Bayanan da BBC ta samu daga garin Mubi na jihar Adamawa na cewa 'yan Boko Haram sun fasa bankunan garin tare da kona babbar kasuwar garin.

Wani mazaunin garin Alhaji Abdurrahman Kwacam ya bayyana cewar a yanzu garin na hannu 'yan kungiyar Boko Haram.

Kwacam ya ce "Sojoji sun gudu daga garin Mubi sannan an kona babbar kasuwa, sun kona Police stations."

Ya kara da cewar "An faffasa bankuna 11 a garin Mubi kuma muna cikin yanayi mara dadi."

Dubban mutane sun fice daga gidajensu domin kaucewa rikicin.

Yanzu haka bayanai na cewa 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kafa tutarsu a garin na Mubi inda suka datse wasu manyan titunan garin.