'Yan Boko Haram sun fatattaki sojoji a Mubi

Yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yan Boko Haram

Rahotanni daga yankin Mubi na jihar Adamawa a arewa maso gabashin Nijeriya, sun nuna cewa mayakan Boko Haram sun fatattaki jami'an tsaron kasar kana suka tilasta wa dimbin mutane barin garuruwansu, bayan da suka kadddamar da hare-hare jiya Laraba inda aka samu hasarar rayuka.

Wasu rahotanni ma sun ce yanzu haka mayakan ne ke iko da garin na Mubi, wanda shi ne gari na biyu mafi girma a jihar ta Adamawa mai makwabtaka da Jamhuriyar Kamaru, bayan da suka fasa gidan yari da wani barikin soja dake garin.

Mazauna garin sun bayyana cewar sun ga gawarwakin mutane da aka kashe a kan tituna.

Karin bayani