Nijar na fama da matsalar karancin Gas

Niger
Image caption mutane da yawa sun shiga mawuyacin hali dalilin karancin gas a Nijar

A jamhuriyar Nijer matsalar karancin Gas na girki ta jefa mutane da dama cikin wani mawuyacin hali.

An dai shafe tsawon lokaci ana fama da matsalar karancin makashin na Gas a cibiyoyin da ake sayar da shi.

To sai dai kuma masu ruwa da tsaki a fannin hadahadar gas din, suna ci gaba da wanke kansu daga wannan matsalar.

Wakiliyar BBC a Damagaram, Tchima Illa Issofou, ta ruwaito cewa akwai iyalai da dama dake amfani da gas wajen aikace aikacen gida a kasar ta Nijar.