Mahara sun kashe sojojin Niger tara.

Shugaba Issoufou na Nijar Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Issoufou na Nijar

Rahotanni daga yankin arewa maso yammacin Nijar na cewa wasu mahara da ake zargin mayakan Mujao ne daga kasar Mali sun kai hari yankin, inda suka kashe sojojin Nijar tara, tare da raunata wasu karin biyar.

Wakilin BBC da ya ziyarci yankunan da aka kai harin, ya ce maharan sun kai hare-hare uku ne a lokaci guda, da asubahin ranar Alhamis inda suka kashe sojoji hudu a sansanin 'yan gudun hijirar 'yan Mali da ke Mangaize, sannan suka kashe wasu sojojin biyar a Zarumdarai, da kuma fasa wani gidan yari a garin Wallam, inda fursunoni 62 suka tsere.

Yankunan da aka kai hare-haren dai na da iyaka da kasar Mali a cikin jihar Tillaberi.