An haramtawa Ferdinand buga wasanni uku

Rio Ferdinand Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyar QPR za ta duba yuwuwar daukaka kara kan wannan hukunci

Hukumar kwallon kafa ta FA a kasar Ingila ta dakatar da dan wasan QPR Rio Ferdinand daga buga wasanni uku.

Wannan mataki ya biyo bayan wani sako da tsohon kyaftin din Ingilan ya aike ne a shafin Twitter wanda ke da alaka da batsa.

Baya ga haka, har ila yau hukumar ta FA ta ci tarar Ferdinand mai shekaru 35 pam din Ingila dubu 25,000.

Sannan an yi mai gargadi kan irin halayensa inda aka bashi shawarar halartar wani shiri na ilimantar da 'yan wasa da hukumar ta FA ke shiryawa na gyara hali.

Mai horar da 'yan wasan QPR, Harry Redknapp ya ce bai yi tsammanin hukuncin zai yi tsauri haka ba, inda ya kara da cewa za su tattauna da hukumomin kungiyar su ga ko za su daukaka kara kan wannan hukunci.