An sauke Shugaba Compaore a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu zanga-zanga sun bukaci Compaore ya sauka

Rundunar soji a kasar Burkina Faso ta ce ta sauke Shugaba Blaise Compaore daga kan karagar mulkin kasar.

Kakakin rundunar ya shaida wa masu zanga-zanga a Ouagadougou, babban birnin kasar cewa a yanzu ba Mr. Compaore ne ke mulki ba.

A ranar Alhamis ne masu zanga-zanga suka cinna wa ginin majalisar dokokin kasar wuta saboda adawa da mulkin Mr Compraore na tsawon shekaru 27.

Tun da farko, Shugaba Compaore ya yi jawabi ga al'ummar kasar, inda ya ce zai sauka daga mukaminsa nan da watanni 12 masu zuwa.