An kai harin bam a Gombe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani likita ya ce an kai musu gawarwakin mutane da dama

Rahotannin da muke samu daga Gombe a arewacin Nigeria na cewa an ji karar bama bamai a wata tashar motar da ake kira Gombe Line.

Mazauna birnin sun shaida wa BBC cewa sun ga gawawwaki bayan harin bam din.

Wani jami'in kiwon lafiya a babban asibitin Gombe ya shaida wa BBC cewa ya ga gawawwaki fiye da goma, kuma dukkansu da kuna a jikinsu.

Haka kuma ya ce ya ga wasu sassan jikin mutane da aka kai asibitin.

Ya zuwa yanzu dai ba a san adadin wadanda suka samu raunuka a sanadiyyar fashewar bam din ba.