Bam ya kashe mutane 8 a Gombe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bam din da ya fashe a tashar mota a Kano

'Yan sanda a jihar Gombe sun ce akalla mutane takwas ne suka mutu sakamakon fashewar bam a tashar mota da ke jihar.

Bayanai sun ce bam din ya fashe ne a cikin wata mota a cikin tashar lamarin da yan janyo jikkatar mutane 32.

Kwamishinan 'yan sanda a Gombe, Abdullahi Kudu Nma ya shaida wa BBC cewar sun damke mutane uku cikin wadanda ake zargi da tayar da bam din.

Wani jami'in kiwon lafiya a babban asibitin Gombe ya shaida wa BBC cewa ya ga gawawwaki fiye da goma, kuma dukkansu da kuna a jikinsu.

Haka kuma ya ce ya ga wasu sassan jikin mutane da aka kai asibitin.

Kawo babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma dai Boko Haram ake zargi saboda ta saba kai hare-haren bam a tashoshin mota a Nigeria.