An bude Masallacin Kudus

Image caption Masallacin Kudus ne na uku mafi daraja a Musulunci

Hukumomin Isra'ila sun sake bude masallacin Kudus bayan rufe shi a ranar Alhamis sakamakon wani rikici da ya taso.

Amma kuma an tura karin 'yan sanda zuwa yankin da masallacin ya ke gabanin sallar Juma'a.

Falasdinawa a birnin Kudus sun yi kira a gudanar da zanga-zanga sakamakon kashe wani bafaladine da wani da dan sanda ya yi.

An zargin mutumin da aka kashe din da harbin wani bayahude, Yehuda Glick.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya bayyana damuwa kan karuwar zaman dar-dar a birnin Kudus.