An fitar da na'urar gwajin motsa jiki da barci

Microsoft Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ana daura na'urar a hanu ne kamin ta yi aiki

Kamfanin Microsoft ya fitar da wata na'ura mai gwajin yanayin barcin mutum da kuma irin motsa jikin da mutum ke yi.

Na'urar wacce ake daura ta a hannu za kuma ta iya bayar da damar yin wasu hada-hada kamar samun kaiwa ga asibitoci ta wayar salula kirar smartphones.

Na'urar a cewar kamfanin na Microsoft za ta iya bin diddigin bugun zuciyar mutum da irin gajiyar dake jikinsa har ma da irin yadda yake shiga rana.

Wannan fasaha itace ta baya-baya nan da kamfanin na Microsfoft ya fitar a fannin kiwon lafiya tun bayan wacce ya kera makamancin wannan a shekarar 2007.

" Wannan zai zamanto kadan daga cikin irin tsare-tsaren da muke da su a shekara a fannin kiwon lafiya." Kamfanin na Microsoft ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar ta email.

Kamfanin ya kara da cewa, a kasar Amurka yake shirin fara fitar da wannan na'ura.

A cewar shugabannin kamfanin ba sa so ne a bar su a baya a irin ci gaban da ake samu a fannoni daban daban na rayuwa.

Yanzu haka an kuma yiwa na'urar kudi kan dalar Amurka 199.