APC ta maida martani kan batun Tambuwal

Shugaban Jam'i'yyar APC Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Jam'i'yyar APC

A Nijeriya babbar Jam'iyyar adawa ta APC ta ce matakin janye jami'an tsaron da ke kare lafiyar kakakin majalisar wakilan kasar, Aminu Tambuwal bayan da ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jamiyyar adawa ta APC bai zo mata da mamaki ba.

Mataimakin shugaban Jam'iyyar APC na kasa mai kula da shiyyar arewacin kasar, Senata Lawal Shu'aibu, ya ce an dade ana ruwa kasa tana shanyewa.

Dangane da matakin da rundunar 'yan sandan Nijeriya ta dauka na janye jami'an tsaron dake kare lafiyar kakakin majalisar, wasu Lauyoyi da suka yi sharhi, sun ce matakin ya saba ma kundin tsarin mulkin Nijeriyar.

Karin bayani