'Abin da ya sa Soji suka tsere daga Mubi'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabannin soji dai sun sha zargin cewa dama wasu sojojin ba don su bauta wa kasa suka shiga soji ba

Wani soja wanda ke cikin sojojin da ke garin Mubi a jihar Adamawa a Nigeria, lokacin da 'yan Boko haram suka karbe garin ya ce rashin makamai ne ya sa sojoji suka janye daga fagen fama.

A wata hira da BBC sojan ya ce ana yaudararsu "Da ma abin da su ke yi kenan sai su yi wa mota fenti, sai ace ga sabuwa nan, muna fara harbi da ita sai ta mutu."

Sojan ya kuma bayyana cewa maharan da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun fi sojojin Najeriya manyan makamai, domin bindiga AK47 ce kawai a hannun sojojin.

Haka kuma ya musanta cewa wasu cikinsu sun shiga aikin soja ne saboda sun rasa aikin yi, yana mai cewa mafi yawa daga cikinsu sun je Liberia da Sudan da ma Krenuwa.

Sojan ya ce muddin aka basu makamai ba a yaudare su ba kamar yadda aka saba ba, za su koma Mubi kuma su fuskanci Maharan.

Ya ce halin da ake da shi ya fara fita daga ransu.