Tsugune bata kare ba a Burkina Faso

Tsohon shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Compaore ya yi muranus bayan shafe shekaru 27 ya na mulki a kasar Burkina Faso.

An samu rarrabuwar kawuna tsakanin Sojojin Burkina Faso, kan ko waye zai jagoranci kasar bayan shugaba Blaise Compaore ya yi murabus daga mukamin sa da ya shafe tsahon shekarau 27 ya na yi.

Kafar yada labaran yankin ta watsa sanarwar da mataimakin babban dogarin shugaban kasar Kanal Isaac Zida ya yi na cewa ya na ganin shi ya dace ya jagoranci kasar.

Tun da fari shugaban hafsan sojojin Kasar Janal Honore Traore ya sanar da cewar shi ne a matsayin shugaban kasa.

Shugaba Compaore ya yi murabus ne a ranar juma'a, bayan kudurinsa na yiwa kundin tsarin mulkin kasar grambawul dan samu damar sake tsayawa takarar a shekara mai zuwa ya ruguje,.

Saboda gagarumar zanga-zangar kin amincewa da hakan da aka yi a kasar.