''Ba mu yi mamakin aurar da 'ya'yan mu ba''

Wasu daga cikin iyayen 'yan matan Sakandaren Chibok da aka sace Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shekau ya musanta batun sasantawa da gwamnatin Nigeria ta sanar ta cimma da kungiyar ta Boko Haram.

Jama'a sun soma tofa albarkacin bakinsu game da sabon Bidiyon da shugaban Kungiyar Boko Haram ya fitar wanda ya karyata maganar tsagaita wuta.

Shugaban al'ummar Chibok mazauna Abuja Dr Pogu Bitrus yace kalaman da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar shekau din ya yi na cewa babu maganar tsagaita wuta, bai zo musu da mamaki ba.

Dr. Bitrus ya kuma ce dama can suna da shakku game da sanarwar tsagaita wutar, da kuma wanda ya ke ikirarin yana magana da yawun 'yan kungiyar.

Game da 'yan matan da Abubakar Shekau yake cewa sun musuluntar da su, kuma an aurar da su kuwa, Dr Bitrus ya ce dama tuni suka ga alamun hakan a wancan bidiyon da kungiyar ta fitar, wanda ya nuna su sanye da hijabai

Mr Bitrus ya ce fatansu yanzu shi ne a gano 'yan matan , ba tare da damuwar ko an musuluntar da su ko kuma basu musulunta ba