Microsoft ya kaddamar da na'urar daurawa a hannu

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Microsoft na son bunkasa fasahar sa a fannin kiwon lafiya

Kamfanin Microsoft ya kaddamar da wata na'ura da ake sanyawa a hannu ta farko da zata iya bibiyar baccin mutum da kuma yadda yake motsa jiki.

Za a sayar da wannan na'ura ta Microsoft a kan kudi $199 a dakin ajjiye kayayyaki na kamfanin dake shafin internet.

Na'urar za ta iya aiki tsawon kwanaki biyu bayan an yi cajin ta.

Tana kuma iya gane bugun zuciyar mutum da yawan kitsen dake jikin dan- Adam da gajiyar dake tattare da mutum da kuma yadda yawan hasken ranar dake ratsa jikin mutum.

Ko a shekarar 2007 kamfanin Mocrosoft ya kirkiro da wata hanya ta kula da lafiya wato HealthVault.

Sauran manyan kamfanonin fasaha kamar Apple da Samsung da Google duka sun kirkiri hanyoyin kula da lafiya kuma suna duba yiwuwar kirkirar wasu na'urori da ake sanyawa a hannu, wadanda bukatarsu ke karuwa.

Sai dai wannan na'ura ta Microsoft ta banbanta saboda tana aiki ne da dukkanin kamfanonin wayar salula da kuma shafukan sada zumunta na facebook da kuma twitter