Jirgin da zai je duniyar wata ya tarwatse

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Richard Branson ya ce zai cigaba da ganin ya cimma burinsa na zuwa yawon bude- ido duniyar wata

Wani jirgin zuwa duniyar wata dake kan gwaji a California ya tarwatse inda matukin jirgin daya ya mutu sannan wani ya sami mummunan rauni.

Virgin Galactic ne yake kirkirar jirgin domin tura masu yawan bude ido zuwa karshen duniyar wata.

Mutane fiye da dari biyar ne suka sanya hannun neman zuwa.

Shugaban Kamfanin Virgin Richard Branson na kan hanyarsa ta zuwa wajen, kuma ya dau alkawarin kaddamar da jirgin da zai rika tafiya duniyar wata zuwa karshen shekara.