Sanarwar tsagaita wuta abin kunya ne - APC

Image caption APC bata gamsu da matakan tsaron da ake dauka a Nigeria ba

A Najeriya, babbar jam'iyyar adawa ta APC ta bukaci da a gudanar da cikakken bincike don gano abin da ta kira yarjejeniyar tsagaita wuta ta bogi da ta ce wasu mukarraban gwamnati suka yi ikirarin cewa sun cimma da kungiyar Boko Haram.

Jam'iyyar APC wacce ke maida martani kan sabon faifan bidiyon da Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar inda ya musanta batun tsagaita wutar, ta ce ikirarin da mukarraban gwamnatin suka yi tamkar yaudarar al'umma ne kuma babban abin kunya ga kasar baki daya.

Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa shiyyar arewacin Nigeria Sanata Lawal Shu'aibu ya yi zargin cewa gwamnatin Nigeria na karya kuma siyasa ce kawai ta sanya cikin maganar.

Ya kuma yi zargin cewa gwamnatin PDP bata daukar shawarar su.