Za a gudanar da gangami a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto Getty

Jam'iyyun adawa da kuma kungiyoyin fararen hula a Burkina Faso sun yi kiran da a gudanar da wani gagarumin gangami a yau Lahadi domin nuna adawa da karbe iko da sojojin kasar suka yi bayan saukar Shugaba Blaise Compoare.

Toshon Shugaban dai yanzu haka yana kasar Ivory Coast.

Jam'iyyun adawar da kuma kungiyoyin fararen hular sun ce kamata ya yi canjin mulkin ya kasance na demokradiya.

A ranar asabar ne rundunar sojin Kasar ta amince da Laftanal Kanal Zida a matsayin sabon Shugaba Kasar.