Ana zanga-zangar kin soja a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto Getty

Masu zanga-zanga a Burkina Faso sun sake hallara a Wagadugu, babban birnin kasar, don nuna adawarsu da karbe mulkin kasar da sojoji suka yi.

Sun yi wa babban dandalin birnin lakabi da 'Dandalin Juyin Juya Hali'.

Jam'iyyun adawa sun ce dole sai dai shugaban farar hula ya jagoranci gwamnatin rikon-kwaryar kasar, har ya zuwa lokacin da za'a gudanar da sabon zaben shugaban kasa.

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a kasar, Mohamed Ibn Chambas, ya jaddada bukatun, yana mai cewa majalisar na bukatar a kaucewa aza ma kasar takunkumi.

A ranar Asabar ne rundunar sojin kasar ta nada Leftanar Kanar Isaac Zida a matsayin shugaban rikon-kwarya, bayan tashin hankalin da ya kawo karshen mulkin Blaise Compaore.

Amurka ta yi Allah wadai da abin da ta kira yunkurin tirsasa wa jama'a.

Karin bayani