Ana ci gaba da musayar yawu a Burkina Faso

Laftanal Kanal Isaac Zida da sojoji suka ayyana a matsayin sabon shugaban kasar Burkina Faso Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojojin kasar sun ayyana Laftanal Kanal Isaac Zida a matsayin sabon shugaban kasa.

Amurka ta yi Allawadai da abinda ta kira yunkurin da sojoji suka yi a Burkina Faso na kokarin karbar mulkin kasar daga hannun fararen hula, bayan juyin juya halin da ya tilastawa shugaba Blaise Compaore yin murabus.

Dakarun kasar sun ayyana Laftanal Kanal Isaac Zida a matsayin sabon shugaban kasar, sai dai ma'aikatar tsaron Amurka ta bukaci sojojin su maida mulkin hannun hukumomin fararer hular Burkina Faso cikin gaggawa, tare da fara shirin gudanar da zabe mai inganci.

Wani mazaunin babban birnin kasar Wagadugu sun bayyana halin da ake ciki a kasar, inda yace barayi na balla gidajen mutane suna sace musu kayayyaki.

Itama tarayyar kasashen Afurka ta yi kiran da a kafa gwamnatin hadaka ta farar hula, a na su bangaren su ma 'yan adawa a kasar sun ce ba za su amince da abinda sojojin suka yi ba, dan haka sun yi kiran da a fito zanga-zanga a yau lahadi.