Sojoji sun yi harbe harbe a Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojoji sun yi harbe harbe domin tarwatsa masu zanga zanga

A Burkina Faso sojoji sun yi harbe harbe domin tarwatsa masu zanga zanga a Ouagadougou babban birnin kasar.

Rahotani sun ce sojojin sun yi harbe harben ne a daidai lokacin da shugabar 'yan adawa Sara Sereme ta isa dandanlin tare da wasu magoya bayanta.

Sojojin sun tarwatsa duban masu zanga zanga a dandanlin birnin kasar inda 'yan adawa ke neman da shugaban rukon kwarya ya kasance farar hulla har zuwa zabe na gaba.

Manzon Majalasar Dinkin Duniya Mohamed ibn Chambas ya yi gargadin saka takunkumi idan sojoji suka tsaya kan mulki.