'Yan gudun hijira 10,000 sun kwarara Yola

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hare haren wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne ya sa dubban jama'a sun tsere zuwa Yolan Adamawa

A Nigeria rahotanni daga jahar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar na cewa 'yan gudun hijira sama da dubu goma ne su ka yi tururuwa zuwa Yola babban birnin jahar.

Yawancin 'yan gudun hijirar na kokarin gujewa hare haren tashin hankalin 'yan kungiyar Boko Haram ne domin su tsira da rayukansu.

To sai dai wata matsala da ake fuskanta ita ce ta rashin abinci da kuma muhali ingantace da 'yan gudun hijirar ke kokawa da ita.

'Yan bindigar da ake zargin 'yan Boko Haram sun kaddamar da munanan hare hare a wsau garuruwan jahar Adamawan abinda ya tilastawa jama'a tserewa daga wadannan garuruwa zuwa Yola babban birnin jahar.

Hukumar bada agajin gaggawa ta ce tana iyakacin kokarinta wajen taimakawa 'yan gudun hijirar wajen basu kayan abinci da na kwanciya.