An nuna damuwa kan dokar leda a Nijar

Hakkin mallakar hoto

A Jamhuriyar Nijar, bayan da majalisar dokokin kasar ta kafa dokar hana shiga da leda a kasar, wasu kungiyoyin kare hakkin masu amfani da kayan masarufi da na 'yan kasuwar ledoji, sun fara nuna damuwarsu.

Sun ce dokar za ta sa mutane da dama su rasa aikin yi.

Sai dai ma'aikatar kare muhalli ta ce gwamnatin za ta bai wa 'yan kasuwar wa'adin watanni shidda don su samu su shigar da ledar da suka riga suka yi oda.

Haka nan kuma za'a wayar da kawunan jama'a akan fa'idar dokar.