Virgin Galactic ya kare kansa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jirgin na gwajin zuwa duniyar wata

Virgin Galactic ya hakikance cewa kula da lafiyar jirgin shine babban aikin da ya sa a gaba, bayan hatsarin jirginsa dake kan gwaji a Amurka a ranar Jumu'a

Kamfanin ya ce akida yake sanyawa a gaba kafin ya yanke duk wata shawara a shekaru goman da suka gabata, kuma duk wani abu sabanin haka ba gaskiya bane.

Jirgin Virgin Galactic mai niyyar zuwa duniyar wata dai ya fashe ne a sararin samaniya a lokacin da yake kan gwaji a hamadar Mojave dake California, inda matukin jirgin guda ya mutu.

Shugaban hukumar kula da tsaron sufuri ta Amurka (NTSB) Christophe Hart ya ce har yanzu ba a san musabbabin hatsarin jirgin ba, amma ya kara da cewa masu bincike sun gano wata matsala dangane da wata na'ura da ke cikin jirgin

Ya ce tankunan man jirgin na zuwa duniyar wata guda biyu da kuma injinsa basu nuna cewa akwai matsala ba

Masu binciken NTSB a yanzu sun gano kusan dukkanin sassan jirgin da ya tarwatse a wani bangare na wani bincike da za'a dauki wata da watanni kafin ya kammalu.

'Zamu kalli batutuwan da suka shafi horo, zamu kalli al'adar kula da tsaron lafiyar jirgin' in ji Mr Hart

Ya kara da cewa 'muna da batutuwa da dama da zamu kalla kafin mu ce ga dalilin faduwar jirgin'

Mutumin da ya kirkiro Virgin Galactic Sir Richard Branson ya ce a shirye yake ya gano abinda ya faru, sannan ya koyi darasi daga wannan musifa da ta afka musu

Virgin Galactic na fatan kaddamar da jirgin zuwa duniyar wata a shekarar 2015.

Tuni ya karbi kudaden fasinjoji fiye da 700 a kan dala dubu dari biyu da hamsin kowanne fasinja, inda Richard Branson ya sha alwashin kasancewa cikin tafiyar a jirgin farko da zai je duniyar watan