Kotu ta hana yunkurin katse hutun 'yan majalisa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana ci gaba da cece-kuce kan sauya shekar da Tambuwal ya yi.

Wata kotun tarayyar a Abuja ta bayar da umurnin dakatar da 'yan majalisar wakilai na jam'iyar PDP daga yunkurin da suke na sake kiran zaman majalisar daga hutun da take yi.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan da 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar APC suka shigar da kara suna neman kotun da ta hana gwamnatin tarayya da jami'anta daga kiran majalisar daga hutu har sai ranar 3 ga watan Disamba.

Bayan ya sauya sheka zuwa APC daga PDP, a ranar 28 ga watan Oktoba ,Shugaban majalisar wakilan, Alhaji Aminu Tambuwal, ya dage zaman majalisar har ya zuwa ranar 3 ga watan Nuwanba.

Sai dai rahotanni na cewa wasu 'yan majalisar na jam'iyyar PDP na kokarin katse hutun majalisar domin su sami damar tsige kakakin.