Microsoft ya kawo karshen sayar da Windows 7 da 8

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Za a maye gurbin Windows 7 da 8 da Windows 10

Microsoft a hukumance ya daina sayar da kwafi kwafi na manhajar Windows 7 da 8.

An sanya ranar daina manhajar a wani lokaci a baya kuma zai taimakawa Microsoft sa mutane su soma amfani da sabbin manhajoji na yadda kamfanin ke aiki.

A waje guda kuma, alkaluma sun nuna cewa mutane na janyewa daga amfani da tsofaffin manhajoji na Windows.

A yanzu za'a bullo da wanda ake kira Windows 10 wanda za'a saka a karshen shekarar 2015.

Daga ranar 31 ga watan Oktoba, masu sayayya ba zasu iya sake sayen manhajoji na Windows 7 da kuma Windows 8 ba.

Wadannan canje- canje sun shafi dukkanin kwafi kwafi da aka sayo a shaguna ko kuma wadanda aka saukar akan kwamfitoci.

Wannan sauyin da aka samu ka iya daukar lokaci kafin ya samu karbuwa a kasuwa saboda mutane da dama na da tsofaffin manhajojin Windows kuma za su cigaba da sayar da kwamfitocin dake dauke da manhajojin.