Bam ya hallaka 'yan Shi'a 21 a Yobe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daruruwan 'yan Shi'a a lokacin muzahara a Kano

Rahotanni daga garin Potiskum na jihar Yobe a Nigeria na cewa an kai hari a kan wasu 'yan shi'a da ke bukin Ashura inda mutane 21 suka rasu.

Shugaban 'yan shi'a a jihar Yobe, Mustapha Lawan Nasidi ya ce an kashe musu mutane 21 sannan wasu kuma 50 sun samu raunuka.

Ya kuma yi zargin cewar dakarun tsaro sun je wurin kuma suka bude musu wuta.

Kawo yanzu dakarun tsaron Nigeria ba su maida martani ba.

Garin Potiskum na daga cikin wuraren da 'yan Boko Haram ke kai hare-hare a jihar ta Yobe.

'Yan Boko Haram sun hallaka dubban mutane a Nigeria musamman a yankin arewacin kasar.