Kwale-kwale ya nitse da mutane 24 a Turkiya

Image caption An ci gaba da aikin ceto domin zakulo mutane

Wani karamin jirgin ruwa da ke dauke da 'yan ci-rani ya nitse a tekun Bahar Aswad, kusa da birnin Santanbul na Turkiyya, inda ya hallaka mutane akalla 24.

Jiragen ruwa da na sama, da masu saukar ungulu na masu aikin ceto, na ta aikin neman sauran mutanen da suka bace.

Kimanin 'yan ci-rani 40 yawancinsu kananan yara ake ganin suna cikin jirgin lokacin da ya kife da safiyar ranar Litinin.

Ba a tabbatar da kasashensu yawancin mutanen ba amma rahotanni sun ce wasunsu 'yan Syria ne.

Wani wakilin BBC, ya ce Turkiyya daya ce daga cikin tashoshin da 'yan ci rani da ke kokarin shiga kasashen Tarayyar Turai suke tashi.