An ji karar harbe-harbe a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Nigeria na fuskantar matsin lamba kan 'yan Boko Haram

Mazauna birnin Maiduguri sun wayi gari da jin karar harbe-harbe da kara mai karfi a ranar Talata abinda ya sa suka shiga cikin zullumi kan ko 'yan Boko Haram sun kai hari ne a cikin birnin.

Sai dai wata majiya a jami'an tsaro Nigeria ta shaidawa BBC cewar dakarun kasar ne suka yi gwajin makamai domin tsoratar da masu tada kayar baya shiga cikin birnin na Maiduguri.

Majiyar ba ta yi karin haske ba game da ko 'yan Boko Haram na shirin kaddamar da hari a cikin Maiduguri ne ko kuma a'a.

A cikin 'yan watannin nan 'yan Boko Haram sun kwace iko da garuruwa da dama a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Wannan al'amari na kara zaman zullumin da ake ciki a wasu manyan biranen arewa maso gabashin Nigeria.