Poroshenko ya nemi a soke wasu dokoki a Ukraine

shugaba Poroshenko na Ukraine Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption shugaba Poroshenko na Ukraine

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko, ya yi kira ga majalisar tsaro da ta dokokin kasar tasa su soke wata doka da ta ba da matsayi na musamman ga yankuna biyu da suka balle suka kuma ayyana ikon cin gashin kansu a gabashin Ukraine.

Lokacin da yake magana kafin fara zaman majalisar tsaron, Mr Poroshenko, ya kuma ce, ya umarci kwamandojin sojinsa su aika sabbin rundunonin soji da za su kare duk wani hari da 'yan tawaye da Rasha ke mara wa baya za su kai a birni na biyu mafi girma a Ukraine, wato Kharkiv da tashar jirgin ruwa ta Mariupol.

Shugaba Poroshenko ya dauki wannan matakin ne bayan da 'yan tawayen suka yi zabe ranar Lahadi a yankunan da suka balle tare da ayyana ikon cin gashin kansu, a matsayin jamhuriyar Donetsk da ta Lugansk.

Tun farko , Ukraine da kasashen Yammacin Duniya sun yi watsi da zaben , Rasha kuwa ta amince da shi.