Katsina: Hare hare na sa mutane yin kaura

Nigeria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matasan garin Shimfida sun ce za su zauna su kare mahaifarsu

Rahotanni daga jihar Katsina na cewa jama'ar garin Shimfida na yin gudun hijira zuwa garin Jibya sakamakon hare hare da wasu 'yan bindiga ke kaiwa garin.

Bayanai sun kara da cewa a yanzu haka, gaba daya mata da dattijai da yara sun koma Jibiya, yayin da matasa ne kawai suka rage da sunan kare garin na su.

"Mu gaskiya mu anan aka haife mu nan kuma za mu mutu." In ji wani matashi a garin na Shimfida.

A yanzu haka dai an ce an jibge jami'an tsaro, yayin da ake cikin fargabar karin wasu hare haren 'yan bindigar.