Farashin mai ya yi mummunan faduwa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan Julin da ya wuce ana sayar da danyen man a kan $100 ne

Farashin danyen man fetur ya yi mummunan faduwar da ba a ga irinta ba a cikin shekaru hudu, bayan da Saudiyya ta rage farashin man da take sayarwa Amurka a ranar Talata.

Hakan dai ya shafi kasuwar danyan man da ke tangal-tangal, amma akwai yiwuwar ragin ya yi ba zata wajen ceto tattalin arzikin duniya.

Ragin da aka samu na kashi 25 cikin dari na farashin man tun lokacin bazara ka iya bunkasa kudaden da jama'a ke kashewa da zuba jari a harkar kasuwanci a bangarorin tattalin arziki da dama na duniya, yayin da kudin sayen mai ya ragu.

Sai dai kasashen da ke hako mai kamar Rasha da Venezuela, wadanda suke kashe makudan kudade wajen hako mai, kuma kasafin kudinsu ya dogara a kan tsadar makamashi, za su yi asara.

Haka kuma farashin mai sauki zai iya janyo raguwar bunkasar samar da kayayyaki a Amurka, wanda hakan zai shafi moriyar da jama'a da kuma harkokin kasuwanci za su ci na ragin farashin man.

Farashin danyen man a Amurka ya fadi da kashi biyu a ranar Talata, inda ya kai $77.19, a wani sa'in ma ya kai $75.84, farashi mafi karanci tun bayan watan Oktoban 2011.

Farashin danyen mai na Brent da aka shata a kasuwannin duniya ya yi kasa da kashi biyu da digo uku zuwa $82.82, inda a baya ma ya taba kai wa $82.08 farashi mafi karanci a shekaru hudu.