Nawaz Sherif ya yi martani kan kisan kiristoci

Hakkin mallakar hoto n
Image caption An zargi mamatan ne da wulakanta Alkur'ani mai tsarki

Firai ministan Pakistan, Nawaz Sherif, ya bayyana kisan wasu ma'aurata Kirista da wasu Musulmi suka yi a matsayin muguntar da ba za a amince da ita ba.

A ranar Talata ne aka yi wa mutanen biyu dukan-kawo-wuka har suka mutu, a wani karamin gari da ke da nisan kilomita sittin daga birnin Lahore.

Mr. Sherif ya ce gwamnati ba za ta amince mutane su dauki doka a hannunsu ba.

Hakan ya biyo bayan wata zanga-zanga da kiristoci 200 suka yi a birnin Lahore, suna kira da ayi garonbawul kan dokar batanci na kasar.