Man City na fuskantar barazanar ficewa

Man City Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ya zama dole Man City ta doke Bayern kana ta yi nasara akan Roma

Kungiyar Manchester City na fuskantar barazanar ficewa daga gasar cin kofin zakarun turai bayan da CSKA Moscow ta doke ta da ci 2-1.

Bayan ga cewa ta sha mamaya, alkalin wasa ya sallami 'yan wasanta Fernandinho da kuma Yaya Toure daga filin wasa.

Hakan dai na nufin 'yan wasan ba za su buga wasan su a nan gaba da Bayern Munich wadda za ta karbi bakuncin wasan.

Yanzu haka City ba ta yi nasarar wasa ko guda ba kuma ya zama mata dole ta doke Bayern a karawarsu sannan ta yi nasar akan Roma a gidanta idan har ta na so ta ci gaba da kasancewa a gasar.