Ana taron ECOWAS kan Ebola, Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Kaow yanzu cutar Ebola ta kashe mutane 4,800 a Yammacin Afrika

Shugabannnin kasashen kungiyar tattalin arziki na Afrika ta Yamma, ECOWAS ko kuma CEDEAO sun hallara a birnin Accra na kasar Ghana domin taron gaggawa na yini biyu.

Manyan batutuwan da taron zai duba sun hada da yadda za a shawo kan cutar Ebola da ke ci gaba da hallaka mutane a wasu kasashen yammacin Afrika.

Shugabannin kasashen za su kuma duba hanyoyin sulhunta rikicin siyasar Burkina Faso, inda sojoji suka kifar da gwamnatin Blaise Compaore a karshen makon da ya gabata.

Taron na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da Ebola, Tony Banbury , ya ce ba shi da kudade da kuma kayan aikin yaki da cutar.

Shugaban wanda ya ziyarci kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo da ke fama da annobar a Yammacin Afrika, ya ce ana bukatar karin taimako.

Karin bayani