ICC ba za ta hukunta Isra'ila ba

Jirgin ruwan Mavi Marmara Hakkin mallakar hoto AFP

Kotun hukunta miyagun laifuka ta duniya, ICC, ta ce ba za ta dauki mataki ba game da kutsen da sojin kudumbalar Isra'ila suka yi a kan wani jirgin ruwan Turkiyya ba .

Jirgin ruwan na cikin tawagar jiragen ruwan da ke kan hanyarsu ta zuwa yankin Zirin Gaza na Falasdinawa lokacin da aka yi musu kutsen, shekaru hudu baya.

Kotun ta ce kisan da aka yi wa 'yan kasar Turkiyya takwas da kuma wani Ba'amurke haifaffen kasar ta Turikya da ke cikin jirgin ruwan na Mavi Marmara bai kai ya zama wata gamsasshiyar shaida da za ta sa a ci gaba da bincike a kan lamarin ba.

Duk da cewa kotun ta ICC ta yi amanna mai yiwuwa Israilar ta aikata laifukan yaki.