Dubban beraye sun addabi asibiti a Indiya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu aiko da rahotanni sun ce ba a tsaftace yawancin asibitocin gwamnati a Indiya

Wani babban asibiti a Indiya ya ce yana kokarin ganin ya magance matsalar dubban berayen da suka addabe shi.

Kamfanin da aka bai wa kwangilar kawar da berayen ya shaida wa BBC cewa, sun ga dubban ramukan da berayen suka yi a kasan asibitin na Maharaja Yeshwantrao da ke Madhya Pradesh.

A halin yanzu dai kamfanin na zuba abinci mai guba ga berayen.

Haka kuma kamfanin ya ce ya taba kashe dubban beraye a asibitin shekaru 20 da suka wuce.